Gwamnatin tarayya ta sanar da wani shiri na samar da cibiyoyin canza man gas (CNG) da kuma gidajen mai a manyan makarantun gwamnatin tarayya 20 a fadin Najeriya.
Kara karantawaMa’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Boriowo Folasade, ta sanar da kaddamar da wani shiri na koyar da fasaha da koyar da sana’o’in hannu (TVET) a duk fadin kasar domin bunkasa sana’o’i da suka dace da masana’antu a Najeriya.
Kara karantawaKaramin Ministan Ayyuka, Muhammad Goronyo, a wata ziyara da ya kai Katsina a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa wasu manyan tituna guda biyar a Katsina na daga cikin hanyoyin da gwamnatin tarayya ta yi tanadin kasafin kudi domin kammalawa.
Kara karantawaBabban Daraktan Hukumar Kididdiga ta Jihar Katsina, Farfesa Sani Saifullahi Ibrahim, ya yi alkawarin samar da ingantattun kididdiga na jihar Katsina.
Kara karantawaDakta Abdulhakim Badamasi, likita ne a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya Katsina, ya shawarci jama’a da su rika zuwa asibitin domin duba lafiyar koda a kai a kai domin kaucewa kamuwa da cutar a makara.
Kara karantawaHukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bai wa kamfanin Max Air damar ci gaba da gudanar da ayyukanta na cikin gida bayan da hukumar ta gudanar da wani bincike mai zurfi kan tsaro da tattalin arziki.
Kara karantawaBabban Alkalin Alkalan Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya shawarci masu hannu da shuni da su yi amfani da dukiyarsu wajen taimaka wa marayu da marasa galihu a tsakanin al’umma.
Kara karantawaSanarwar da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Katsina ta fitar.
Kara karantawaA wata sanarwa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana kame tare da gurfanar da wasu mata da miji, Baba Sule Abubakar Sadiq da Hafsat Kabir Lawal tare da wasu mutane biyu bisa laifin damfarar ma’aikacin ofishin canji.
Kara karantawaKatsina Football Academy ta fitar da sunayen ‘yan wasa 16 da aka zabo domin shiga Kwalejin a shekarar 2025.
Kara karantawa