Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 ya zama doka

Da fatan za a raba

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudurin kasafin kudi na shekarar 2025 na sama da naira biliyan 698 na ayyukan gwamnatin jihar da kuma naira biliyan 184 na ayyukan kananan hukumomi 27.

Hakan ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton zaunannen kwamitin kasafin kudi na majalisar.

Da yake gabatar da rahotan shugaban kwamitin wanda shi ne mamba mai wakiltar mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya bayyana cewa dukkanin kwamitocin majalisar sun tantance tanade-tanaden kasafin kowace ma’aikatar da hukumar domin yin gyara ko kari a cikin kasafin kudin.

A cewarsa, kwamitocin sun kuma yi da masu ruwa da tsaki daban-daban da suka hada da kungiyoyin farar hula tare da gudanar da aikin tantancewa a kokarin da ake na isa ga wani cikakken daftarin kasafin kudi domin gabatar da shi ga zaman majalisar.

Bayan amincewar baki daya ta hanyar kada kuri’a, kakakin majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 ya zama doka.

  • Labarai masu alaka

    Hukumar NSITF reshen Katsina ta yi bikin Ranar Lafiya ta Duniya tare da Mai da hankali kan AI da Digitalization

    Da fatan za a raba

    Hukumar Inshorar Inshora ta Najeriya (NSITF) reshen jihar Katsina ta bi sahun takwarorinta na duniya domin bikin ranar lafiya ta duniya ta 2025.

    Kara karantawa

    Gov yayi alƙawarin haɓaka KYCV, ya kafa ƙarin cibiyoyi 10 na Skills.yayin da Federal Polytechnic Daura ke gudanar da taro karo na biyu

    Da fatan za a raba

    Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ilimin fasaha da na sana’a a matsayin mafita ga matsalar rashin aikin yi ga matasa.

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Labarai daga Jihohi

    Labaran Hoto: Koyarwar Aikin Jarida da Tsaro A Garin Kebbi

    Labaran Hoto: Koyarwar Aikin Jarida da Tsaro A Garin Kebbi

    Sama da Zawarawa 220, Karancin Gata Suna Samun Kayan Abinci, Kunshin Ramadan A Kwara

    Sama da Zawarawa 220, Karancin Gata Suna Samun Kayan Abinci, Kunshin Ramadan A Kwara
    0
    Bayyana tunanin ku kuma sami bayanai kyautax
    ()
    x