
Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamma, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya gwamnan jihar Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, Malam Muhammadu Inuwa Yahaya murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Gwamna Radda ya bayyana Gwamna Yahaya a matsayin jagora na kwarai wanda jajircewarsa na ci gaban yanki da hadin gwiwar jihohi ke ci gaba da karfafa ci gaban Arewacin Najeriya baki daya.
Gwamna Radda ya yabawa takwaransa na jihar Gombe bisa hangen nesa da yake jagoranta na kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, inda ya bayyana cewa, iya kokarinsa na ciyar da gwamnonin Arewa kai ga cimma muradun ci gaba daya kara habaka hadin gwiwar yankin a muhimman batutuwa da suka hada da tsaro, ilimi, noma, da samar da ababen more rayuwa.
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Katsina, ina taya mai girma gwamna murnar wannan rana ta musamman, jagorancin ku na kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ya samar da hadin kai, da samar da hanyoyin magance matsalolin hadin gwiwa, da kuma ciyar da muradun yankin mu gaba daya.”
Ya yaba da yadda gwamna Yahaya ke tafiyar da harkokin mulki a zahiri da kuma sadaukar da kai wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Gombe da ma yankin Arewa baki daya.
Gwamna Radda ya yi addu’ar Allah ya karawa Gwamna Yahaya lafiya, hikima da kuma jagorar Ubangiji yayin da yake jagorantar duk jihar Gombe tare da daidaita ayyukan ci gaban yankin ta hanyar kungiyar gwamnonin jihohin Arewa.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
9 ga Oktoba, 2025
