
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Katsina, Alhaji Lawal Haruna Yaro ya ce ginshikan kasafin kudi guda hudu ne.
Alhaji Lawal Haruna wanda ke wakiltar karamar hukumar Musawa a majalisar dokokin jihar ne ya bayyana haka a wani taron kwana daya da kungiyar ‘City Partipation Against Corruption Initiative’ ta shirya a dakin taro na sakatariyar kungiyar NUJ ta jihar Katsina.
Alhaji Lawal Yaro ya bayyana cewa Pillars guda hudu sun hada da rabon da gwamnatin tarayya ke bayarwa, kudaden shiga na cikin gida IGR, karbar jari da kuma tallafin Aids.
Tun da farko Babban Daraktan C-PAC-I Kwamared Bashir Dauda Sabuwar Unguwa ya ce taron kwana daya ya ba matasa damar tattaunawa kan aiwatar da kasafin kudin Jihar Katsina, aiki da kuma tantance Tasiri daga shekarar 2024 zuwa yau.
Kwamared Bashir Dauda ya ce taron ya bai wa ‘yan kasa da ke son sanin yadda kasafin kudin 2025 ke gudana.
A yayin taron wakilin ma’aikatar kasafin kudi, Umar Haruna da shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina AbdulRahman Abdullahi Dutsinma sun yi jawabi kan aiwatar da kasafin.


