
Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta haramta duk wani shagulgulan dare a fadin jihar, saboda tsarin addinin Musulunci da kuma kiyaye kyawawan dabi’u.
Aminu Usman, babban kwamandan Hisbah na Katsina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Katsina, inda ya ce dole ne a rufe duk wani gidan rawa da dare domin dakile munanan dabi’u, da kare mutuncin al’umma, da magance matsalolin tsaro a jihar.
Ya ce hukumar ta sanar da hukumomin tsaro da abin ya shafa, ciki har da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, da su aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata, domin hukumar ta yi gargadin cewa masu karya doka za su fuskanci hukunci mai tsauri.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ta yi gargadin cewa wadanda suka karya doka za su fuskanci hukunci mai tsauri, an umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken bin wannan umarni.
“Mun himmatu wajen gina al’umma ta gari da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Katsina.
“Wannan yunkuri ya yi daidai da kokarin da Hisbah ke yi na ganin mazauna yankin sun ci gaba da rayuwarsu bisa ka’idojin addini da na dabi’a.”