Gwamna Uzodimma, Buni, Barau Sun Jagoranci Tawagar Shugaban Kasa Don Ta’aziyya Ga KTSG Kan Rasuwar Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati Abubakar Lawal Bagiwa
Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Malam Dikko Umaru Radda, ya karbi tawagar shugaban kasa mai karfin iko karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Shugaban Kungiyar Gwamnonin Ci Gaba kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma; da Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, a ziyarar ta’aziyya da suka kai Jihar Katsina kan rasuwar tsohon Mataimakin Babban Kwamandan Kwastam, Alhaji Abubakar Lawal Bagiwa (Sarkin Fulanin Hamcheta).
Kara karantawa



