Gamayyar kungiyoyin farar hula sun roki gwamnatin Katsina da ta sa baki kan jinkirin EHR a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar

Da fatan za a raba

Gamayyar kungiyoyin farar hula ta jihar Katsina tayi kira ga Gwamna Dikko Umar Radda kan ya duba yadda za’a inganta tsarin amfani da Internet wajen gudanar da aikace-aikacen kiwon lafiya a manyan asibitocin jihar Katsina.

Wannan na a cikin wata takarda ne mai dauke da Sa Hannun Shugaban Kungiyar Malam Abdul Rahman Abdullahi Dutsinma wanka aka aikoma Madubin Katsina.

A cewar wannan Takarda wannan ya biyo bayan ziyarar gani da ido da gamayyayar kungiyoyin ta kai a wasu asibitocin tare da ganin yadda marassa lafiya ke faman jira a asibitocin kafin su samu kulawa sakamakon tsaiko da akan samu wajen yin amfani da tsarin Internet domin duba lafiyarsu.

Duk da yake akwai amfani da yawa tattare da tsarin wanda kuma yasa dole a jinjina ma gwamnati kan kawo tsarin, Gamayyar kungiyoyin na shawarartar gwamnati da ta duba yadda zata inganta tsarin ta yadda za’a kara karfin Internet din da kuma duba yiwuwar maida tsarin ya yi aiki lokacin da network ya dauke da yadda aikin zai iya hawa idan network ya dawo.

Wannan zai taimaka wajen rage dogon jira da wahalhalun da marassa lafiya ke fuskanta a asibitocin.

  • Labarai masu alaka

    KTSG Abokan Kungiyoyi masu zaman kansu na Belgium akan Maganin Ciwon daji na Mata

    Da fatan za a raba

    Gwamnatin jihar Katsina ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa reshen kasar Belgium mai suna Revive, domin bayar da ayyukan jinya da horas da mata masu fama da cutar kansar nono da mahaifa a jihar.

    Kara karantawa

    Gwamna Radda ya taya Farfesa Joash Ojo Amupitan murnar nada shugaban hukumar INEC

    Da fatan za a raba

    Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) murnar amincewar majalisar dokokin jihar baki daya a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Labarai daga Jihohi

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025

    Sama da Al’ummomin Ifelodun LG 100 A Kwara Suna Samun Ayyuka

    Sama da Al’ummomin Ifelodun LG 100 A Kwara Suna Samun Ayyuka
    0
    Bayyana tunanin ku kuma sami bayanai kyautax
    ()
    x