Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar litinin 16 ga watan Satumba 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Da yake sanar da hakan a madadin gwamnati, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da kuma kasashen waje murna, inda ya ce, “Ina taya al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar wannan rana.
Dokta Tunji-Ojo ya bukaci al’ummar Musulmi da dukkan ‘yan Najeriya da su rungumi “ruhun hakuri, sadaukarwa, da juriya”. Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da ci gaba.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
“Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya al’ummar musulmin gida da na kasashen waje murnar wannan rana.
“Dr. Tunji-Ojo ya bukaci al’ummar Musulmi da kuma ‘yan Najeriya da su yi koyi da ruhin hakuri, sadaukarwa, da juriya.
“Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana, Ministan ya roke su da su yi amfani da damar da suka samu wajen yin addu’o’in samun dawwamammen zaman lafiya da kuma samar da daidaito a tsakanin al’umma.”