Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ayyana yau Litinin 8 ga watan Yuli, 2024, daidai da 2 ga watan Al-muharram, 1446, a matsayin ranar hutun jama’a domin tunawa da sabuwar shekara ta Musulunci.
Gwamna Dikko Radda ya ce an ayyana ranar Litinin a matsayin ranar kyauta ta aiki domin baiwa dukkan ma’aikata da ke jihar damar hada kai da sauran al’ummar Musulmi domin murnar shiga sabuwar shekara (1446 bayan Hijirar Annabi Muhammad SAW daga Makkah zuwa Madina).
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari, gwamnan ya taya daukacin al’ummar musulmin jihar da ma duniya murnar shiga sabuwar shekara da ta fara a ranar Lahadi 1 ga watan Al-muharram 1446.
Malam Dikko Radda ya bukaci al’ummar musulmi da su yi riko da koyarwar manzon Allah (SAW) a cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya yi amfani da damar da ya samu wajen yin kira ga malamai da su ci gaba da yin nasiha ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar da kuma addu’ar Allah ya kawo mana dauki kan kalubalen tsaro da wahalhalun da ake fuskanta a kasar nan.