Kashi na farko na alhazan jihar Kebbi, sun isa filin jirgin saman Ahmadu Bello International Airport Birnin Kebbi da yammacin ranar Asabar daga filin jirgin sama na Sarki Abdulazeez dake Jedda.
Jirgin mai suna flynas ya sauka filin jirgin ne da misalin karfe 9:42 na dare tare da alhazai 330 ciki har da jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar.
Dukkanin mahajjatan suna cikin koshin lafiya sai dai wasu da sanyi da tari suka shafa sakamakon shan ruwan sanyi da na’urar sanyaya iska a lokacin da suke kasa mai tsarki.
Kashi na farko da suka isa Najeriya su ne na farko da aka fara jigilar su daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar 15 ga watan Mayun 2024 a yayin kaddamar da jirgin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya yi a Birnin Kebbi, jihar Kebbi.