Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira da a kara tura jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa al’ummar Eruku da ke karamar Hukumar Ekiti domin dakile sabbin hare-haren da ake kai wa yankin nan take.
Gwamna AbdulRazaq ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar jim kadan bayan ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar da abin ya shafa.
Ya nemi a gaggauta tura karin jami’an tsaro domin tallafawa tsarin tsaro da ke yankin.
Gwamna AbdulRazaq ya yi Allah wadai da harin, kuma yana tausayawa mutanen Eruku da kewaye, musamman iyalai da kuma CAC da harin ya shafa kai tsaye.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro don magance wadannan kalubale da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Gwamnan, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan tura karin sojoji 900 don karfafa tsaro a jihar.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa karin sojojin za su samar da karin kariya, da kuma cikakken tsaro ga jama’a, da kuma kawo kwanciyar hankali na dindindin, ga al’ummomin da abin ya shafa.






