
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kaddamar da shirin raya yankin Renewed Hope Ward, inda ya bayyana shi a matsayin wani shiri na shiga tsakani da ya yi daidai da tsarin ci gaban talakawan jihar Katsina da ta fara aiki a watan Nuwamba 2024.
Gwamna Radda ya bayyana jin dadinsa da yadda gwamnatin tarayya ta dauki irin wannan tsarin na shirin cigaban al’ummar jihar Katsina (KSCDP), wanda ke samun sakamako mai kyau a fadin mazabun jihar 361.
“Mun ji dadin yadda mai girma shugaban kasa ya amince da kawo sauyi na ayyukan ci gaba a matakin unguwanni. Abin da muka bullo da shi a jihar Katsina a matsayin dabarun karfafawa jama’a a yanzu haka ana ci gaba da bunkasa a kasa baki daya ta hanyar shirin ci gaban Renewed Hope Ward,” in ji Gwamna Radda.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar Katsina ta fitar da Naira biliyan 3.6 a watan Nuwamba 2024 domin fara shirin ci gaban al’umma, inda aka ware Naira miliyan 10 ga kowane gundumomin zabe 361 na jihar ta hanyar asusu na kananan hukumomi.
Ya kara da cewa shirin ya inganta hadin kan al’umma, karfafa tattalin arziki, daidaiton jinsi, samar da ababen more rayuwa, da dorewar muhalli a fadin jihar Katsina.
Gwamna Radda ya yaba wa Shugaba Tinubu kan shawarar tsawaita wannan abin koyi a fadin kasar ta hanyar shirin raya fatan alheri na Renewed Hope Ward, wanda ya shafi sama da ‘yan Nijeriya miliyan 8.8 a fadin sassan zabe 8,809.
“Kwarin gwiwar da shugaban kasa ya yi na ganin an samar da ci gaba zuwa mataki mafi kankanta domin bunkasa harkokin tattalin arziki, samar da ayyukan yi, rage radadin talauci, da inganta samar da abinci, ya dace da abin da muke yi a jihar Katsina. Wannan hadin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jihohi da na tarayya zai sa a gaggauta kawo sauyi daga tushe,” inji shi.
Gwamnan ya tabbatarwa da Tinubu na jihar Katsina a shirye yake na hada kai da gwamnatin tarayya wajen aiwatar da shirin raya Renewed Hope Ward, tare da yin amfani da gogewar jihar da darasin da aka koya daga KSCDP.
Gwamna Radda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, inda ya ba da tabbacin cewa jihar Katsina za ta ci gaba da jagoranci ta hanyar samar da ribar dimokuradiyya ga al’umma kai tsaye.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
12 ga Oktoba, 2025

