
- Yana danganta tasowar yaran da ba su zuwa makaranta da kuma rashin kula da iyali
- Shugaban majalisar Daura, kwamishinan harkokin addini, da shugaban hukumar zakkat sun yi alkawarin bada goyon baya
- Malamai sun yi alkawarin bayar da jagoranci da hadin kai kan bitar dokokin iyali a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya danganta karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma karuwar munanan dabi’u a Arewacin Najeriya da rashin kulawar iyaye da gazawar iyalai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na gida.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yau yayin wani zama na tattaunawa da shugabannin Majalisar Malamai da shugabannin hukumar Zakka da Wakafi, wanda aka gudanar a Sakatariyar Majalisar da ke Katsina.
Gwamna Radda ya jaddada cewa kafa tsarin doka mai karfi da inganci na da matukar muhimmanci wajen gina zaman aure mai dorewa, da ayyana nauyin da ke wuyan iyaye, da samar da kwanciyar hankali na iyali. Ya bukaci malamai da su fara tuntubar juna ta hanyar shigar da malaman addinin musulunci a fadin jihar domin samar da abubuwan da za su kawo gyara a dokar iyali.
Gwamnan ya kuma shawarci iyaye da su kasance masu taka-tsan-tsan ta hanyar binciko halaye da tarihin masu neman auren kafin su aurar da ‘ya’yansu mata.
Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, ya bada tabbacin cewa majalisar a shirye take ta samar da dokokin da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da kuma karfafa rayuwar iyali a jihar. Ya ce tuni hukumomi irin su Hukumar Zakka da Wakafi da Hukumar Hisbah ke tunkarar wasu matsalolin da suka addabi jihar.
Kwamishinan ma’aikatar addini Alhaji Ishaq Shehu Dabai, ya bayyana bukatar yin cikakken bincike wajen magance rikice-rikicen iyali, musamman wadanda sukan kai ga rabuwar aure. Ya jaddada cewa matakan kariya da daidaita sabani na da matukar muhimmanci wajen kare rayuwar iyali.
Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi Dr. Ahmed Abdullahi Filin Samji, ya yi kira da a samar da wata sabuwar doka da ta tilasta yin gwajin kwayar cutar kanjamau kafin aure. Ya kuma ba da shawarar cewa garambawul ya kamata ya karfafa shayar da jarirai nonon uwa zalla domin rage rashin abinci mai gina jiki da sauran kalubalen lafiyar yara.
Sauran mahalarta taron da suka hada da Alkali Muhammad Yusuf, da Malam Musa Abubakar Kankia, da Aliyu Harazumi Danja, da Malam Aminu Abdullahi Yammawa, sun yi magana kan illar rabuwar iyali ga yara da al’umma. Sun shawarci Majalisar Malamai da ta tuntubi malamai masu daraja a fadin Najeriya domin ci gaba da ba da jagoranci kan gyaran da ake shirin yi.
An kammala taron ne da sabon alkawari daga masu ruwa da tsaki na karfafa tsarin iyali, da inganta hakki na iyaye, da kuma magance matsalolin da ke haifar da munanan dabi’u da rikicin ‘ya’yan da ba su zuwa makaranta a jihar Katsina.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
23 ga Satumba, 2025









