
Yanzu haka Mukaddashin Gwamna Malam Faruk Lawal Jobe ne ke jagorantar taron majalisar tsaro na gaggawa a fadar gwamnatin jihar Katsina. Ana ci gaba da zaman.
Taron dai ya hada manyan shugabannin hukumomin tsaro a jihar da suka hada da wakilai daga rundunar soji, jami’an tsaro, daraktan tsaro na jihar (DG SS), kwamishinan ‘yan sanda, mai kula da shige-da-fice, kwamandojin tsaron farin kaya, kwastam, da kiyaye hadurra, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, da kuma manyan malaman addini.
Tattaunawar da aka yi a wajen taron sun mayar da hankali ne kan matsalolin rashin tsaro da dabarun tabbatar da tsaro da ci gaban al’ummar jihar Katsina.