
Kungiyar manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) reshen jihar Kwara na taya Dr. Afeez Abolore murnar sake masa aiki a matsayin kwamishinan noma da raya karkara.
A wata sanarwa da kodinetan RIFAN na jihar Mallam Mohammed Salihu ya fitar ta ce tura shi ma’aikatar zai kara karfafa dabarun da aka dauka na inganta samar da abinci a jihar.
Ya ce kwamishinan ya mallaki kwarewar da za ta baiwa gwamnatin jihar damar cimma burinta na tabbatar da wadatar abinci.
Mallam Mohammed yace gudunmawar da Dr.Abolore ya bayar a tsohuwar ma’aikatar ma’adanai za ta yi masa jagora wajen mayar da sabuwar ma’aikatar domin samun ingantaccen aiki.
Sanarwar ta yabawa gwamnan jihar bisa goyon bayan sauye-sauye da yawa da kuma kokarin tabbatar da samar da abinci a jihar.
Sanarwar ta bukace shi da ya kwaikwayi dabarun tattalin arziki daban-daban da aka yi amfani da su a tsohuwar ma’aikatar don tabbatar da ingantaccen aiki a fannin.
Yana ba da tabbacin ’yan kungiyar RIFAN su goyi bayan kokarinsa na daukar ma’aikatar noma da raya karkara zuwa wani babban mataki.