Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina Alh. Bala Abu Musawa Ya Jagoranci Mika Tutar Takara Ga Ƴan Takarar Kansilolin Mazaɓu Goma Na Ƙaramar Hukumar Jibiya

Da fatan za a raba

A ranar Laraba 29/1/2025 mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alh. Bala Abu Musawa, tare da Ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Jibia Hon. Surajo Ado, suka jagoranci miƙa tutar takarar ga ƴan takarar Kansilolin mazaɓu goma na ƙaramar hukumar ta Jibia.

Bayan kammala miƙa tutocin, mataimakin shugaban jami’iyyar APCn na jiha Alh. Bala Abu Musawa, ya gabatar da jawabin shi a wurin taron, inda ya fara da nuna farin cikin sa da Allah SWT ya nuna mashi wannan rana mai matuƙar muhimmanci wacce za’a miƙa wannan tutoci ga yan takarar ƙaramar hukumar da ma wasu ƙananan hukumomin kamar yadda uwar jam’iyyar ta jiha ta umarta

Ya cigaba da cewa” na baro ƙaramar hukumar ta musawa na taho Jibia mussaman saboda miƙa wannan tutoci ga ƴan takarar wannan ƙaramar hukuma domin aminci da ke tsakani na da al’ummar ƙaramar hukumar Jibia.

Dan gane da Ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar kuma Hon. Surajo Ado, nasan mutumin kirki ne sabo da ina da tabbacin ƙaramar hukumar Jibia tana daga cikin ƙananan hukumomin da suka dace Ɗan takara, sabo da munyi aiki tare lokacin da yake shugaban jam’iyyar wannan ƙaramar hukumar.

Ina da tabbacin Hon. Surajo Ado, ba zai bada kunya ba, an fiddo mutumin kirki wanda zai ciyar da ƙaramar hukumar Jibia gaba.

Shima a nashi jawabin, Ɗan takarar shugaban Hon. Surajo Ado, ya yi godiya ga al’ummar ƙaramar hukumar Jibia akan ƙauna da soyayya da suke nuna mashi, inda ya basu tabbacin gudanar da shugabanci na adalci wanda kuma zaiyi ƙoƙarin kawo abubuwan cigaba a ƙaramar hukumar.

Tun da fari da yake bayyana maƙasudin taron shugaban Jami’iyyar APC na ƙaramar hukumar Jibia Hon. Nasiru Al’mustapha Danye, ya bayyana cewa kamar yadda uwar jam’iyyar ta jiha ta bada umarni na ƙaddamar da wannan taro a kowace karamar hukuma, mu ma yau mun taru ne domin miƙa wannan tuta ga yan takarkarun mu na kansiloli domin basu damar fara gudanar da yaƙin neman zaɓe.

Mutane da dama ne su ka tofa albarkacin bakinsu yayin taron gangamin bada tutar ga ƴan takarar kansilolin.

Daga ƙarshe kamar yadda ya saba jagoran jam’iyyar ta APC ya karɓi wasu ‘ƴaƴan jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC, sabo da gamsuwa da suka yi da salon mulkin gwamnan jihar katsina Malan Dikko Umar Radda PhD.

Taron bada tutar ya samu halar manyan masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar, ƴan uwa da kuma abokan arziki.

  • Labarai masu alaka

    Kanwan Katsina ya taya sabon shugaba murna

    Da fatan za a raba

    Kanwan Katsina kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara, mni, ya taya sabon shugaban karamar hukumar Kankara, Honorabul Kasimu Dan Tsoho Katoge murnar rantsar da sabon shugaban karamar hukumar, bayan rantsar da shi a hukumance da gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi a hukumance.

    Kara karantawa

    ‘Yan Jarida Da Suka Kai Ziyara Suna Yabawa Gwamna Nasir Idris…Domin Sa Mutane A Gaba

    Da fatan za a raba

    ‘Yan jaridun da suka ziyarci Katsina, Zamfara, da takwarorinsu na Kebbi mai masaukin baki, wadanda ke halartar wani shiri na horaswa a Birnin Kebbi, sun dauki lokaci mai tsawo don ziyartar wasu muhimman ayyuka na gwamnatin jihar Kebbi.

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Labarai daga Jihohi

    Labaran Hoto: Koyarwar Aikin Jarida da Tsaro A Garin Kebbi

    Labaran Hoto: Koyarwar Aikin Jarida da Tsaro A Garin Kebbi

    Sama da Zawarawa 220, Karancin Gata Suna Samun Kayan Abinci, Kunshin Ramadan A Kwara

    Sama da Zawarawa 220, Karancin Gata Suna Samun Kayan Abinci, Kunshin Ramadan A Kwara
    0
    Bayyana tunanin ku kuma sami bayanai kyautax
    ()
    x