Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da masu aikata miyagun ayyuka a jihar ba.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban kwamandan runduna ta takwas (GOC) da kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Arewa maso Yamma, Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, a wata ziyarar ban girma da suka kai gidan gwamnatin jihar Katsina.
Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnati za ta iya yin sulhu da ‘yan bindigar ne kawai a kan wasu sharudda da aka gindaya don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, ya kara da cewa tattaunawar za ta iya yin nasara ne kawai idan an samu cikakkiyar karbuwa da shigar al’ummomin da abin ya shafa.
Gwamnan ya bayyana cewa an kafa kwamitin masu ruwa da tsaki don tabbatar da shigar da al’umma cikin ayyukan samar da zaman lafiya, tare da bayyana budaddiyar goyon bayan tuba na gaskiya da sake hadewa.
“’Yan bindiga ‘yan uwanmu ne da aka haifa a cikinmu, amma sun zabi su zama masu laifi, wadanda da gaske suka mika wuya suka kuma nemi sake gina rayuwarsu za su samu goyon bayan gwamnatinmu,” Gwamnan ya ba da tabbacin.
Gwamnan ya kara da cewa “Mun shirya samar da kayan aiki don sake dawo da su da kuma kula da kiwo, wanda zai ba su damar zama masu amfani a cikin al’umma.”
Gwamna Radda ya kara tabbatar da zuba jarin da jihar Katsina ta yi a fannin samar da tsaro, wanda ya zarce jihohi da dama a tarayyar Najeriya.
Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ba da tallafin kayan aiki don magance kalubalen samar da man fetur da kuma ci gaba da gudanar da aikin.
Gwamna Radda ya yaba wa kwamandojin runduna na musamman da na Brigade, yana mai bayyana hakan a matsayin abin koyi ta hanyar jagorantar ayyuka da kuma nuna kwazo.
Gwamnan ya jaddada cewa, wannan kokari tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya, sojojin sama, rundunar ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaron farin kaya, da kuma Katsina Community Watch Corps, sun samar da ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar.
“Yanzu manoman mu za su iya noma gonakinsu da kai amfanin gonarsu zuwa kasuwa,” in ji Gwamna Radda.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Wannan ci gaba na zahiri ya nuna ingancin dabarun tsaro na hadin gwiwa.”
Tun da farko, Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose ya bayyana cewa ya je jihar Katsina ne a ziyarar aikin sa na kwata na farko a duk jihohin da ke karkashin runduna ta 8 da ta hada da Katsina da kuma tattaunawa da gwamnatin jihar, sabuwar rundunar ‘Operation Safe Northwest’ da ta kaddamar.
“Wannan shiri na da nufin hada kan al’umma, inganta ayyukan tsaro da samar da zaman lafiya mai dorewa,” in ji shi.
Manjo Janar Ajose ya kuma lura cewa babban hafsan sojin ya rubutawa jahohin hudu na shiyyar kan abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan, musamman rahotannin wasu ‘yan bindiga da ke nuna sha’awar zaman lafiya. “Yana da mahimmanci a bayyana cewa sojojin Najeriya ba sa tattaunawa da masu aikata laifuka ko ‘yan fashi, mun himmatu wajen lalubo hanyoyin da za a bi don magance wannan kalubalen na ci gaba da daurewa,” in ji shi.
Sai dai GOC ya nuna godiya ga Gwamna Radda kan yadda ake ci gaba da tallafawa ayyukan tsaro a jihar. Manjo Janar Ajose ya ba da misali da fitar da kudade don ci gaba da aiki na Forward Operating Base (FOB).
Taron ya samu halartar mataimakin gwamna Malam Faruk Jobe, shugaban ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, Alh. Abdullahi Aliyu Turaji Babban Sakataren Gwamnan Jihar da wasu ‘Yan Majalisar Zartarwa na Jiha.