Masarautar Daddara Ta Bada Kyautar ‘Ya’ya Masani

  • ..
  • Babban
  • January 2, 2025
  • 0 Comments
Da fatan za a raba

Kungiyar Cigaban Al-ummar Masarautar Ɗaddara ta Gudanar da Taron Karramawa ga Wasu Muhimman Mutune da Suka Fito daga Masarautar

A rana laraba 01-01-2025, ƙungiyar ta karrama wasu muhiman mutune da suke bada gudummuwa da taimakon al-ummah da ke cikin masarautar dama ƙaramar hukumar Jibia, a ɗakin taro na hukumar ma’aikatar ƙananan hukumomi da ke Katsina.

Da yake gabatar da jawabin sa shugaban ƙungiyar Hon. Halilu Buhari Kanwa, yace mun shirya wannan taron domin karrama wasu muhiman mutune da suka bada gudunmuwa da dama wajen cigabab al’umma ta ɓangarori da dama kama daga ilimi, taimakon marassa lafiya, samarwa matasa aikin yi, samar da ruwan sha da dai sauransu.

Shugaban ƙungiyar ya yaba ma mai girma gwamnan jihar Katsina akan ƙokarin da yake na ingata rayuwar al’ummar jihar Katsina.

A nashi jawabin shugaban ƙaramar hukumar Jibia wanda ya samu wakilcin sakataren ƙaramar hukumar, ya yaba ma kungiyar wajen karrama wanan mutune wanda kowa ya san irin gudummuwar da suke badawa a masarautar Ɗaddara da ma ƙaramar hukumar Jibia baki ɗaya.

waɗan da aka karramar sun haɗa da Hon. Shafi’u Abdullahi shugaban kula da ɗakunan karatu na jihar Katsina, Alh Lawal Sulaiman, Alh Abdullahi Riko, Alh Ibrahim Isah, Dakta Lawal Ishiye, da dai sauran su.

Da yake gabatar da jawabin sa a madadin waɗan da aka karrama ɗin shugaban ɗakunan karatu na jihar Katsina Hon. Shafiu Abdullahi, yayi godiya ga Allah da ya nuna masu wanan rana ta karamawa da akayi musu, ya kuma jinjinawa ƙungiyar a bisa ƙoƙarin ta na kawo ci gaba a yankin nasu.

Taron ya samu halartar Wakilin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Hakimin Ɗaɗɗara Alh. Usman Usman Nagogo, Hakimin Kaita Yazeed Abdulkarim, ƴan uwa da abokan arziki.

  • .

    Labarai masu alaka

    GWAMNA NAMADI YA NADA MASU BAKI NA MUSAMMAN GUDA BIYAR

    Da fatan za a raba

    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da nadin karin masu ba da shawara na musamman guda 5.

    Kara karantawa

    Mutuwar Shugaban Miyetti Allah: ‘Yan sanda sun fara farautar wadanda ake zargi

    Da fatan za a raba

    Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun fara gudanar da bincike kan lamarin a ranar Asabar din da ta gabata a kauyen Mairana da ke karamar hukumar Kusada a jihar Katsina wanda ya yi sanadin mutuwar shugaban kungiyar Miyetti Allah, Surajo Rufa’i.

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Ka Bace

    GWAMNA NAMADI YA NADA MASU BAKI NA MUSAMMAN GUDA BIYAR

    GWAMNA NAMADI YA NADA MASU BAKI NA MUSAMMAN GUDA BIYAR

    Mutuwar Shugaban Miyetti Allah: ‘Yan sanda sun fara farautar wadanda ake zargi

    Mutuwar Shugaban Miyetti Allah: ‘Yan sanda sun fara farautar wadanda ake zargi
    0
    Ina son ra'ayoyin ku, da fatan za a yi sharhi.x
    ()
    x