
An yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa marayu da marasa galihu a cikin al’umma.
Alh Isah Musa wanda ya jagoranci tawagar ma’aikatar ya ce, sun kasance a cibiyar domin yabawa tare da karfafa gwiwar daliban da suka tsunduma cikin sana’o’i domin dogaro da kai.
Kwamishinan ya yi karin haske kan mahimmancin koyon sana’o’i tare da jaddada bukatar cibiyar ta tabbatar da ingancin kayayyaki, a cewarsa ana shirin yin kwangilar dinkin kayan Sallah ga wasu zababbun marayu a jihar.
Ya ce shi da sauran kungiyoyin bayar da agaji za su hada kai don ganin an sake duba marayu da marasa galihu domin inganta rayuwarsu.
Kwamishinan ya kuma bukaci mahalarta taron da su rubanya kokarinsu da kuma dogaro da kai domin yin alfahari da ayyukan tattalin arzikin jihar da ma kasa baki daya.