Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada muhimmancin shirin karfafa gwiwa wajen magance rikice-rikice domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaba.
Gwamna Malam Dikko Radda wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ma’aikatar mata, Hajiya Hadiza Abubakar Yar’adua, ta taya wadanda suka ci gajiyar shirin murnar kasancewa cikin wadanda aka amince da su ci gajiyar shirin.
Hajiya Hadiza Yar’adua ta bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan karimcin ta hanyar da ta dace domin bunkasa zamantakewar tattalin arzikin yankunansu.
Da yake magana a madadin Cibiyar Dimokuradiyya da Ci gaban CDD, Mista David ya ce shirin karfafawa wani bangare ne na ayyukan jin kai daga Cibiyar.
Mista David ya bayyana cewa wadanda suka amfana 100 sun fito ne daga kananan hukumomin Batsari, Danmusa, Jibia da Kankara domin su samu sana’o’in dogaro da kai.
A wata tattaunawa da suka yi da wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun nuna godiya ga CDD bisa wannan karimcin tare da bayar da tabbacin yin amfani da kayayyakin cikin adalci.
Kayayyakin ƙarfafawa sun haɗa da injin niƙa da famfo, injin ɗin ɗinki, kayan aikin gona, walda da kayan aikin kafinta da sauransu.