Shugaban kasa ya nada Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri’s daga jihar Katsina a matsayin sabon kodinetan sabuwar kawance don ci gaban Afirka, NEPAD.
Masu fatan alheri dai sun yi ta tofa albarkacin bakinsu ga wanda aka nada cewa ya dace da wannan aiki, inda suka yaba wa shugaban kasa kan yadda ya dauki wani daga jihar Katsina a kan irin wannan matsayi mai daraja tare da tabbatar da cewa wanda aka nada ba zai yi wa shugaban kasa rai ba.
Daga cikin wadanda suka taya sabon kodinetan NEPAD da aka nada akwai babban daraktan hukumar kula da dakin karatu ta jihar Katsina Shafii Abdu Bugaje.
Babban Darakta na Hukumar Laburare ta Jihar Katsina, yana yi wa sabon kodinetan NEPAD fatan Allah ya yi masa jagora a kan sabon nadin nasa.