Jihar Katsina na daga cikin gwamnatocin jihohi uku da har yanzu ba su fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa N70,000 ba, sauran jihohin sun hada da Cross River, da Zamfara yayin da wasu jihohi suka amince tare da fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na kasa.
KatsinaMirror a baya ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, wanda aka shirya gudanarwa daga yanzu duk wata ya tabbatar da cewa an kafa kwamitin da zai tsara hanyoyin aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan ya ce, “Akan batun sabon mafi karancin albashi, gwamnatin jihar ta himmatu wajen aiwatar da shi, domin an kafa wani kwamiti mai karfi da zai tsara hanyoyin aiwatar da shi a jihar.
A halin da ake ciki, kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta sanya wa’adin yajin aikin da ta shirya gudanarwa a ranar Litinin 1 ga watan Disamba a duk jihohin da ba a aiwatar da mafi karancin albashin ma’aikata ba.
Yanzu haka Jihohi 33 da Babban Birnin Tarayya (FCT) sun bi dokar mafi karancin albashi na kasa na 2024.
Wasu Jihohin da suka hada da Legas da Ribas sun amince su biya sama da Naira 70,000, inda Legas ke ba da mafi girman albashi a kan N85,000.
Ma’aikata a jihohin Akwa Ibom, Enugu, Oyo, da Neja za su samu Naira 80,000, yayin da jihohin Delta da Ogun suka amince da Naira 77,000. Sauran jihohi kamar Ebonyi, Osun, Benue, da Kebbi sun sanya mafi karancin albashin N75,000; Ondo akan N73,000; Kogi da Kaduna akan Naira 72,000; sai Kano da Gombe akan Naira 71,000.
Abia, Adamawa, Anambra, Jigawa, Borno, Edo, Kwara, Nasarawa, Taraba, Ekiti, Bauchi, Yobe, Imo, Plateau, da FCT sun amince da Naira 70,000.
A Kuros Riba kungiyoyin kwadago na neman a biya su N70,000 kuma sun yi kira da a shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a ranar Litinin 24 ga watan Nuwamba.
Kungiyoyin NLC da TUC ne suka shirya yajin aikin bayan wani taro da suka yi a ranar 18 ga watan Nuwamba tare da kwamitin aiwatar da albashin ma’aikata na gwamnatin jihar ya gamu da cikas.
Kungiyoyin kwadagon dai sun ji takaicin sanarwar da Gwamna Bassey Otu ya bayar a ranar 1 ga watan Mayu na cewa za a fara biyan sabon albashin ne a kan Naira 40,000, saboda rashin kudi a jihar.
A halin da ake ciki, ma’aikata a jihar sun yi fatan samun karin albashi kamar yadda aka gani a wasu jihohi kamar Edo, Legas, da Ribas.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gregory Ulayi, shugaban kungiyar NLC a Kuros Riba, ya ce kungiyar za ta ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani idan gwamnatin jihar ta ki aiwatar da albashin N70,000.
Ya bayyana yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a matsayin kira da a dauki mataki, yana mai jaddada cewa idan tattaunawar ta ci tura, kungiyar za ta zafafa zanga-zangar zuwa yajin aikin gama gari.
Sai dai babban sakataren yada labarai na gwamna Otu, Nsa Gill, ya mayar da martani inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti domin tattaunawa da shugabannin kwadago a wani yunkuri na karshe na kaucewa yajin aikin.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na kokarin ganin ta aiwatar da albashin N70,000, tare da yiyuwar sama da wannan adadi.
Hakazalika, gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin samun ci gaba a kokarinta na aiwatar da albashin N70,000.
Rahotanni sun bayyana cewa babban mataimaki na musamman ga gwamna Dauda Lawal Mustafa Jafaru Kaura ya ce jihar ta kafa wani kwamiti da zai yi aiki da cikakken bayanin yadda ake aiwatar da aikin kuma za ta bayyana albashin da zarar kwamitin ya kammala ayyukansa.
Kaura ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatan Zamfara za su karbi sabon albashi nan ba da jimawa ba, inda ya bayyana kudirin gwamnan na inganta albashin ma’aikata, inda ya ce a baya ya kara albashin jihar daga N18,000 zuwa N30,000.