An zabi Comrade Alhassan Yahaya a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya.
Wakilinmu Aminu Musa Bukar da ke Owerri babban birnin jihar Imo ya ruwaito cewa Alhassan, tsohon mataimakin shugaban kungiyar na kasa, ya doke abokin hamayyarsa, Ma’ajin nan mai ci Dele Atunbi, a taron wakilan kungiyar NUJ karo na 8, da aka gudanar a Owerri. babban birnin jihar Imo.
Alhassan, tsohon shugaban karamar hukumar Gombe ta NUJ ya samu kuri’u 436, Atunbi ya samu 97 yayin da Mohammed Garba ya samu kuri’u 39.
Haka nan mataimakiyar darakta a gidan rediyon Najeriya Misis Abimbola Oyetunde ta zama mataimakiyar shugaban kungiyar ba tare da hamayya ba yayin da Misis Ronke Afebioye Samo daga majalisar dokokin jihar Ekiti aka sake zabenta a matsayin mataimakiyar shugabar shiyyar B.
Shima Muhammad Tukur daga jihar Kebbi ya sake zabar mataimakin shugaban shiyyar A, ba tare da hamayya ba, sannan Abdulrazak Bello Kaura daga jihar Zamfara ya sake zaben sakataren kungiyar na shiyya A ba tare da hamayya ba.