Sanata ‘Yar’Adua Ya Tallafawa Manoman Rani a Dutsin-Ma

Da fatan za a raba

A karo na biyu cikin kasa da mako biyu Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua ya tallafawa manoman ban ruwa a karamar hukumar Dutsin-ma ta jihar Katsina.

Ya tallafa musu da takin zamani da injinan fanfo da feshi.

Sanata ‘Yar’aduwa wanda ke rike da sarautar gargajiya ta Mutawallen Katsina shi ne Sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar dattawan tarayyar Najeriya.

Shi ne kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji sannan kuma shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.

Idan dai za a iya tunawa, kasa da mako biyu Sanata ‘Yar’adua ya raba wa manoman noman rani na Dutsin-Ma buhunan taki.

Malam Zailani Muhammad Jikan Maigari ko’odinetan Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua wanda ya wakilci Sanata a yayin taron ya bayyana cewa manufar tallafawa manoman noman ita ce inganta noman ban ruwa a karamar hukumar Dutsin-Ma. Malam Zailani Muhammad ya tuna cewa ko a lokacin noman damina Sanata ‘Yar’aduwa ya samar da taki kyauta ga manoman yankin, ya kara da cewa baya ga bunkasa noma a yankin.

Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’aduwa ya samar da fitilun titi masu amfani da hasken rana da aka sanya a babban asibitin Dutsin-ma da manyan titunan garin domin inganta tsaro a yankin. Sanatan ya kuma horas da wasu matasa a yankin kan sanya hasken rana domin su zama masu dogaro da kai.

Manoman ban ruwa da suka ci gajiyar wannan karimcin sun nuna godiya ga Sanatan tare da bukace shi da ya gyara musu madatsar ruwa da ta lalace a shekarun baya sakamakon ambaliyar ruwa.

A madadin manoman da suka amfana, shugaban karamar hukumar Dutsin-Ma Hon. Sada Ibrahim Sada da mamba mai wakiltar karamar hukumar Dutsin-Ma a majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Abubakar Muhammad Khamis wanda ya yi magana ta bakin wakilansu ya godewa Sanatan kan ayyukan ci gaban karamar hukumar Dutsin-Ma da jihar Katsina baki daya.

Sun bayyana Sanatan a matsayin nagartaccen wakilin jama’ar sa tare da rokonsa da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da yake.

  • Labarai masu alaka

    KTSG Abokan Kungiyoyi masu zaman kansu na Belgium akan Maganin Ciwon daji na Mata

    Da fatan za a raba

    Gwamnatin jihar Katsina ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa reshen kasar Belgium mai suna Revive, domin bayar da ayyukan jinya da horas da mata masu fama da cutar kansar nono da mahaifa a jihar.

    Kara karantawa

    Gwamna Radda ya taya Farfesa Joash Ojo Amupitan murnar nada shugaban hukumar INEC

    Da fatan za a raba

    Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) murnar amincewar majalisar dokokin jihar baki daya a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Labarai daga Jihohi

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025

    Sama da Al’ummomin Ifelodun LG 100 A Kwara Suna Samun Ayyuka

    Sama da Al’ummomin Ifelodun LG 100 A Kwara Suna Samun Ayyuka
    0
    Bayyana tunanin ku kuma sami bayanai kyautax
    ()
    x