An Fara Gasar Kwallon Kafa ta Matasa ‘Yan Kasa da Shekaru 18 ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu Buga na Biyu a Filin Wasan Kwallon Kafa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina Mal Dikko Umaru Radda ya fara gasar a lokacin bikin bude gasar da ta kunshi jihohin Katsina da Bauchi.
Gwamnan, wanda kwamishinan wasanni da ci gaban matasa, Aliyu Lawal Zakari ya wakilta, ya yi maraba da dukkan jihohin da suka shiga gasar zuwa gidan karimci da tarihi.
Gwamnan ya bayyana gasar a matsayin wata hanya ta bunkasa hazaka, wasanni, da kyakkyawar dangantaka tsakanin jihohin da suka shiga gasar.
Radda ya tabbatar wa gwamnatin jihar shirye take ta ci gaba da daukar nauyin gasar da kuma daukar nauyinta a Jihar Katsina domin karawa kokarin gwamnatin tarayya wajen bunkasa kwallon kafa daga matakin farko.
A jawabinsa ga manema labarai, shugaban YSFON na kasa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, wanda mataimakin shugaban Arewa maso Yamma, Aminu Ahmed Wali ya wakilta, ya yaba da kokarin da gwamnatin Jihar Katsina ta yi na daukar nauyin gasar karo na biyu.
Dr. Gawuna ya sake jaddada shirin tabbatar da adalci tsakanin dukkan jihohin da suka shiga gasar tun daga farko har zuwa karshen gasar.
Wasan farko ya ƙare da kwallaye biyu da babu a raga, wanda hakan ya bai wa ƙungiyar YSFON ta Bauchi nasara.









