








Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a yau ya bi sahun takwarorinsa gwamnonin Najeriya a wajen taron kwamitin zartarwa na majalisar sarakunan Najeriya (NCTRN), wanda aka gudanar a Legas.
Taron mai taken “Cibiyar Gargajiya: Mahimmancin shigar da ita cikin ingantaccen shugabanci da inganci a Najeriya,” ya hada manyan sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati daga sassan kasar nan.
Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin gargajiya da na gwamnatoci uku don tinkarar kalubalen tsaro, inganta hadin kai, da ci gaban kasa baki daya. Mahalarta taron sun jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa a matsayin manyan abokan hadin gwiwa a fannin gudanar da mulki, wanzar da zaman lafiya, da kawo sauyi daga tushe a fadin Najeriya.
Babban taron ya gudana ne karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Ooni na Ife, Mai Martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II.
Shugaban kungiyar, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya samu wakilcin gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba, Sanata Hope Uzodinma. Haka kuma akwai shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Alhaji AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara.
Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Babajide Sanwo-Olu na Legas, Usman Ododo na Kogi, Nasir Idris na Kebbi, Ahmad Aliyu na Sokoto, Mai Mala Buni na Yobe, Bassey Otu na Cross River, Monday Okpebolo na Edo, da Abiodun Oyebanji na Ekiti, da dai sauransu.