





Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a yau ya ziyarci masallacin Juma’a mai shekaru 35 da ke Sabon Layi, a kan titin Dutsinma a garin Kankia.
Ziyarar dai ita ce duba halin da masallacin ke ciki, wanda ya dade yana zama cibiyar ibada da tarukan al’umma. Gwamna Radda ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar halin da take ciki, ya kuma jaddada bukatar gyara cikin gaggawa.
Ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen tallafa wa wuraren ibada da kuma samar da amintattun wurare masu kyau ga ‘yan kasa domin gudanar da ayyukansu na addini.
A cewarsa, gyaran da aka shirya zai taimaka wajen kiyaye masallacin da kuma kara karfafa ruhi da zamantakewar al’umma.