


Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya tarbi Abbas Dan-ile Moriki, sabon kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar.
Sake aikin kwamandan Moriki na da nufin karfafa kokarin gwamnati na bunkasa rayuwar al’ummar Katsina.
Gwamna Radda ya tabbatar wa sabon kwamandan goyon bayan gwamnatin jihar ba tare da kakkautawa ba, ya kuma yabawa kungiyar bisa rawar da take takawa wajen yaki da rashin tsaro a fadin jihar.