















A wani bangare na bikin cikar Katsina shekaru 38, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, a jiya ya duba aikin gina tashar iskar Gas/Compressed Natural Gas (LNG/CNG) a cikin birnin Katsina.
Aikin, wanda kamfanin Greenville Energy ne ke daukar nauyi kuma kamfanin distilled Design Concept Limited na gida ne ya aiwatar da shi a filin da gwamnatin jihar Katsina ta kebe domin tallafawa shirin. Haka kuma ma’aikatar wutar lantarki da makamashi da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara a karkashin jagorancin Dakta Hafiz Ahmed, mai ba gwamna shawara na musamman kan wutar lantarki da makamashi ne ke kula da shi.
Da isar Gwamnan ya samu kyakkyawar tarba daga Dakta Hafiz Ahmed tare da injiniyoyin aikin. Bayan ya zagaya wurin, Gwamna Radda ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake tafiya da kuma ingancin aikin, inda ya yabawa ‘yan kwangila da injiniyoyi bisa kwarewa da jajircewarsu.
Ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta samar da makamashi mai dorewa, samar da ayyukan yi, da kuma karfafa tushen masana’antu na jihar. Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatin sa na tallafawa masu zuba jari da kamfanoni na asali don bunkasa koren ci gaba da ci gaba mai dorewa a jihar Katsina.
Gwamna Radda ya samu rakiyar babban sakataren sa Abdullahi Aliyu Turaji; kwamishinan harkokin addini, Alhaji Shehu Dabai; Kwamishinan Lafiya, Dr. Musa Adamu; shugaban karamar hukumar Katsina, Isah Miqdad; da sauran manyan jami’an gwamnati.