
Ya Nanata Alkawarin Karfafa Mata
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafa mata, inda ya bayyana cewa idan aka tallafa wa mata, iyalai da sauran al’umma na kara samun ci gaba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Katsina Ibrahim Kaula Mohammed, kuma aka mikawa Katsina Mirror.
A cewar sanarwar gwamnan ya bayar da tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar hadin kan mata a gidan gwamnati, Katsina.
Tawagar karkashin jagorancin shugabar matan jam’iyyar APC reshen jihar Katsina kuma shugabar kungiyar, Hajiya Binta Husaini Dangani, ta kai ziyarar jajantawa Gwamnan kan harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Gidan Mantau da ke garin Malumfashi, da kuma hadarin da ya rutsa da shi, sun kuma yi amfani da ziyarar wajen jaddada biyayyarsu da goyon bayan gwamnatinsa.
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya gode wa Allah da ya kiyaye rayuka a lokutan kalubalen da aka fuskanta a baya-bayan nan, ya kuma nuna jin dadinsa ga matan bisa nuna kulawa da hadin kai. Ya bayyana mata a matsayin amintattun abokan hadin gwiwa wajen ci gaban al’umma, inda ya tuna da sadaukarwar da suka yi a zabukan da suka gabata.
“Kamar yadda shugabar mata ta nemi wakilcin kashi 50 cikin 100, na yi imanin hakan bai yi yawa ba,” in ji Gwamnan. “Duk abin da mace za ta samu, ta yi amfani da ita don tallafa wa danginta, don haka taimakon mata ya zama wajibi, domin a karfafa su, a karshe muna karfafa al’umma.”
Gwamnan ya ci gaba da bayyana irin ayyukan da ake yi wa mata. Wadannan sun hada da shirin kiwon akuya, wanda ya baiwa mata 10 tallafi a kowace unguwanni 361 na jihar, da kuma shirin tallafa wa mata masu kananan sana’o’i na Ramadan. Ya kara da cewa ana cigaba da aiwatar da wasu tsare-tsare ta ma’aikatar harkokin mata.
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba jihar Katsina za ta kaddamar da shirin tallafawa mata na Najeriya, inda ya bukaci mata da su dauki shirin da muhimmanci da kuma taka rawar gani.
“Idan mata suka rungumi wannan shiri kuma muka yi aiki tare, da yardar Allah, hakan zai taimaka mana wajen magance talauci da ya addabi al’ummarmu, za a gudanar da aikin a kowace unguwa a jihar, kuma da taimakon Allah za ku ga tasirinsa wajen kawo sauyi ga rayuwa,” inji shi.
A karshe ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci da hada kai a shirye-shiryen da suka shafi mata, tare da addu’ar Allah ya jikan tawagar ya kuma koma gidajensu lafiya.
A nata jawabin, Hajiya Binta Husaini Dangani— wacce kuma ke rike da mukamin babbar daraktar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta bayyana cewa kungiyar ta kunshi shugabannin mata daga dukkanin kananan hukumomi 34, da kuma mata ‘yan asalin Najeriya mazauna Katsina. Ta ce kungiyar ta himmatu wajen wayar da kan mata kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Ta bayyana cewa a halin yanzu mata 1,050 ne ke samun horo kan sana’o’i daban-daban, yayin da wasu 100 kuma ke cin gajiyar karin ayyukan karfafawa. A cewarta, tuni mata da dama a fadin Katsina suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati daban-daban.
Ita ma shugabar matan jam’iyyar APC ta jihar, Hajiya Jamila Salam ta jaddada biyayyar mata ga wannan gwamnati mai ci. Ta yi nuni da cewa, kungiyar ta na gudanar da taro da shugabannin mata a matakin kananan hukumomi da kuma gundumomi domin kara bayyana kudirin gwamnati na karfafa mata. Ta roki Gwamnan da ya tabbatar an baiwa mata kashi 50 cikin 100 na wakilci a ayyukan gwamnati.







