






A yau ne shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Katsina suka ziyarci Gwamna Malam Dikko Umaru Radda domin yi masa maraba da dawowar sa daga ziyarar jinya da kuma jajantawa sa bisa afkuwar lamarin Unguwar Mantau.
Tawagar karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar APC na jiha Alhaji Muhammad Sani Ali Daura, ta samu halartar manyan ‘yan jam’iyyar. Ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna biyayya, girmamawa, da goyon bayan Gwamna, yayin da ya kara tabbatar da cewa jam’iyyar APC a Katsina ta ci gaba da kasancewa a dunkule tare da mara baya ga shugabancinsa.
Gwamna Radda ya yaba da ziyarar tare da godewa iyalan jam’iyyar APC da suka ba shi a wannan lokaci.
Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatinsa na kokarin samar da shugabanci na gari, da zaman lafiya, da kuma jin dadin al’ummar Katsina.
Haka kuma akwai mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe; Shugaban ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Nasir Mamman; da Babban Sakatare mai zaman kansa, Alhaji Abdullahi Aliyu Turaji.