





Gwamnan jihar Katsina, Mal. Dikko Umaru Radda ya dawo Najeriya bayan duba lafiyarsa da ya saba yi a kasar waje. Da misalin karfe 1:00 na safe ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport, Abuja, nan take ya wuce Katsina House Abuja.
A gidan Katsina Gwamna Radda ya jagoranci taron tsaro na sirri tare da dukkanin Sanatoci uku masu wakiltar jihar Katsina da daukacin ‘yan majalisar wakilai daga jihar.
Babban taron ya mayar da hankali ne kan kalubalen tsaro da jihar Katsina ke fuskanta a halin yanzu da kuma kokarin hadin gwiwa da ake bukata domin magance su.
Wadanda suka halarci taron sun hada da dukkanin Sanatocin Katsina guda uku, dukkan ‘yan majalisar wakilai ta Katsina, da kuma jam’iyyar APC ta Katsina, Shamsu Sule Funtua.