
Shugaban kwamitin majalisar wakilai akan harkokin soji, Alhaji Aminu Balele Kurfi Dan-Arewa ya jajantawa iyalan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Masarautar Katsina da Daura, da gwamnatin jihar da ma daukacin al’ummar kasar baki daya bisa rasuwar tsohon shugaban kasa.
A cikin sakon ta’aziyyar, Alhaji Aminu Dan-Arewa, ya bayyana rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi ga daukacin kasar da ma al’ummar duniya duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban dimokradiyya da shugabanci na gari.
Alhaji Aminu Dan-Arewa, wanda shi ne mamba mai wakiltar Dutsinma-Kurfi a majalisar dokokin tarayya, ya ce marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da kasancewa a cikin zukatan ‘yan Nijeriya har abada bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa.
Dan majalisar ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Hajiya A’isha Buhari, Leadership of Red and Green Chambers, Malam Mamman Daura, da daukacin iyalan marigayi shugaban kasa da ma Najeriya baki daya bisa rasuwar shugaban kasar nan.
Alhaji Dan-Arewa ya roki Allah SWA da ya gafartawa marigayi tsohon shugaban kasa gajeriyar tafiyarsa, ya karbi kyawawan ayyukansa, ya saka masa da Jannatul Firdausi.