
A kokarinsa na yaki da jahilci da kuma
Kungiyar agaji ta Save the Children ta sha alwashin wayar da kan yara sama da 28,000 da ba sa zuwa makaranta a jihar Katsina ta hanyar shirinta na “Ilimi Ba Ya Jira”.
Manajan shirin na jihar Katsina Altine Lewi ya bayyana haka a lokacin wani taron hadin gwiwa na kungiyar Technical Working Group (TWG), don hada kai da bayar da agajin gaggawa a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da aka gudanar a Mashi.
Altine Lewi ta ce, manufar shirin ita ce a tabbatar da cewa yaran da ba sa zuwa makaranta ko kuma ba su da damar yin karatun boko ba a bar su a baya ba wajen neman ilimin kasashen yamma.
Ta kara da cewa, shirin ya dauki yara sama da 30,000 wadanda ba sa zuwa makaranta da kuma na yara da kuma iyayen yaran da sauran al’umma.
A cewar ta, an ba su kayan koyo da wasu kayan aiki da suka kunshi sabulu, wanka, buroshi, pate hakori, pomade, tissues, wando da sauransu a matsayin kayan tallafi wanda ya jawo hankalin jama’a a cikin shirin.
Ta kuma bayyana cewa, akwai wasu ‘yan kalubale da shirin ke fuskanta amma sun samu nasarar shawo kan su yayin da shugabannin gargajiya da na addini ke ba da hadin kai don samun nasarar shirin.
Save the Children kuma tana aiki tare da gwamnatoci daban-daban da masu ruwa da tsaki na al’umma don ƙarfafa tsarin ilimi da haɓaka ingancin koyo da yanayin koyo.
A nasa jawabin Hakimin Mashi Alhaji Kabiru Ibrahim ya yabawa kokarin kungiyar Save the Children bisa bullo da shirin irin wannan tare da zabar karamar hukumar Mashi a matsayin daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin tare da bayar da tabbacin bayar da cikakken goyon baya da hadin kai domin samun nasarar aikin.
Ya yi kira gare su da su tsawaita shirin zuwa akalla shekaru biyu domin dalibai da dama su amfana, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta yi tanadin da suka dace domin dorewar shirin.
Tun da farko a jawabinsa na maraba sakataren zartarwa na hukumar ilimi ta karamar hukumar Mashi Alhaji Kabiru Aliyu ya ce an fara darussa tun a wasu zababbun cibiyoyi na karamar hukumar.
A cewarsa, an bayar da horo ga malaman sa kai, sannan kuma an baiwa kowane malami alawus na naira dubu 30 domin su samu damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata, ya ce kungiyar Save the Children ta kuma yi shawarwari da sarakunan addini da na gargajiya.
Sarkin ya bukaci malamai da su ba da gudummawar iyaye ga dalibansu wajen ba su mafi kyawun abin da suke bukata don koyo, ya kuma yi kira ga daliban da su kara mai da hankali da muhimmancin karatunsu domin iyayensu da shugabannin al’umma su yi alfahari da su.
Galibin cibiyoyin da suka ziyarta a karamar hukumar Mashi sun nuna sha’awarsu da shirin tare da yaba wa wadanda suka shirya shirin musamman Save the Children tare da bukace su da su fadada shirin domin sauran su amfana.

