
Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Katsina ta raba kayan abinci da kudinsu ya haura naira miliyan hudu da maki bakwai a bana.
Shugaban hukumar Dr. Ahmed Musa Filin Samji ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai nasarorin da hukumar ta samu kawo yanzu tun daga farko har zuwa yau.
Dokta Ahmed Musa ya yi tsokaci sosai kan nasarorin da hukumar ta samu cikin shekaru biyu da kafuwar wannan gwamnati.
Shugaban zartarwar ya bayyana cewa hukumar ta samu damar tattara kayan abinci sama da buhu tamanin da shida da kudinsu ya haura naira biliyan hudu da maki bakwai daga gundumomi arba’in da hudu daga cikin sittin da biyu a masarautar Katsina da Daura.
Ya ci gaba da cewa an raba kayan abincin ga mabukata sama da sittin da takwas da sauran marasa galihu daga cikin nau’ukan mutanen da ke da gata da za a ba su Zakka.
Dr. Ahmed Filin Samji ya ce daga cikin kudaden gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda ya bada naira miliyan ashirin da shugaban kamfanin man Danmarna naira miliyan 22 da sauran attajirai a jihar.