
Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada kudirinta na inganta kanana da matsakaitan masana’antu a fadin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar fasaha da koyar da sana’o’i Alh Isah Muhammad Musa ya bayyana haka a lokacin da yake duba makarantar kaji da kamun kifi da sauran ayyukan noma da aka fi sani da Gidan kwakwa a cikin babban birnin Katsina.
Alh Isah Musa ya ci gaba da cewa, tawagar ma’aikatar ta kasance a makarantar domin tantancewa da kuma alakanta ayyukan makarantar da kuma tsara yadda gwamnati za ta taimaka wajen ci gaba da kyautata rayuwar makarantar.
Kwamishinan wanda ya taya daliban makarantar murnar yaye daliban ya shawarce su da su tabbatar da yin amfani da dukkan ilimin da aka samu domin bunkasa tattalin arziki domin kara samar da ayyukan yi a jihar.
Ya bayyana cewa karni na 21 lokaci ne na samar da damammaki na fasaha don haka akwai bukatar kowa ya rungumi kanana da matsakaitan masana’antu domin ci gaban jihar Katsina da kasa baki daya.
A yayin ziyarar shugaban makarantar Malam Abdulqadir Tukur ne ya zagaya da tawagar kwamishinonin makarantar tare da sauran jami’an hukumar.