
Babban Alkalin Alkalan Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya shawarci masu hannu da shuni da su yi amfani da dukiyarsu wajen taimaka wa marayu da marasa galihu a tsakanin al’umma.
Mai shari’a Musa Danladi Abubkar ne ya bada nasihar a lokacin rabon kayan abinci da nade-nade ga yara marayu da marasa galihu 50 wanda JIBWIS ta shirya wanda aka gudanar a masallacin Juma’a na Kandahar dake kofar Kaura Katsina.
Babban Alkalin, ya yi magana sosai kan muhimmancin taimakawa marasa galihu a tsakanin al’umma Allah ne kadai zai saka wa irin wannan abin.
A nasa jawabin sakataren cibiyar Alhaji Mutar Lawal Tsagem ya bayyana tarihin cibiyar da irin nasarorin da aka samu.
Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da shugaban JIBWIS na jiha, Sheik Dr. Yakubu Musa Hassan, sakataren kwamitin amintattu na cibiyar Engr. Garba Ibrahim Mashi, Imam Sirajo Muhammad Kankia, Sheikh Dr.Haris Isah Dikke, Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir and Executive Secretary SEMA Hajiya Binta Dangani among others .
Kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa, masara, gero da nannade da sauransu.