
An kammala dukkan Shirye-shiryen gasar kawar da shiyya-shiyya na gasar wasannin motsa jiki na kasa da ke tafe a Abeokuta Jihar Ogun.
Daraktan wasanni na jihar Katsina, Alhaji Audu Bello ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Daraktan wasanni ya bayyana cewa, wasanni 68 ne za su wakilci jihar Katsina a gasar da jihohin Arewa maso Yamma za su shiga.
Alhaji Audu Bello ya ce ‘yan wasan jihar za su buga wasan kwallon kafa da kwallon kwando da wasan kwallon raga da na Hockey.
Ya yaba da kokarin Gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa irin goyon bayan da ake ba wa harkokin wasanni a jihar.
Daraktan wasanni ya ba da tabbacin cewa wakilan jihar za su dawo cikin farin ciki bayan kammala gasar.