Ofishin mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Katsina kan harkokin dalibai ya shirya taron shugabannin dalibai na rana daya.
Taron ya gudana ne a dakin taro na Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina, inda ya samu halartar daliban manyan makarantun jihar.
A nata jawabin kwamishiniyar ilimi a matakin farko da sakandire ta jiha Alhaji Isah Muhammad Kankara wanda babban sakatare a ma’aikatar Hajiya Ummulkhairi Bawa ta wakilta ya bayyana taron a matsayin wani ci gaba na maraba da bunkasa tarbiyar hada kan matasa a jihar.
A jawabin maraba mataimaki na musamman kan harkokin dalibai, Alhaji Muhammad Nuhu Nagaske ya ce a yayin taron mahalarta taron za su koyi ilmin ilimi da na aiki.
A wajen taron, Engr. Dokta Muttaqa Rabe Darma, Dokta Mustapha Shehu da Dokta Bashir Isah Waziri, sun gabatar da kasidu kan Haɗin Kan Dabarun Ƙwarewa da Takaddun shaida don Ci gaban Matasa.