Gwamwna Malam Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya yaba da gudummawar da matasan suka bayar a fadin jihar.
Gwamna ya bayyana hakan ne a lokacin taron matasan APC na jihar Katsina da aka gudanar a Katsina.
Gwamna wanda Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar Katsina, Injiniya Sirajo Yazid Abukur ya wakilta ya yaba da hangen nesa na masu shirya taron game da nuna nasarorin wannan gwamnatin.
Tun da farko, mai gabatar da taron, wanda shine Mataimakin Gwamna na Musamman kan Kafafen Yada Labarai na Dijital, Alhaji Abubakar Sani Dan-Abba ya ce taron an yi shi ne don wayar da kan matasa game da nasarorin wannan gwamnatin.
Alhaji Abubakar Dan-Abba ya bayyana cewa a lokacin taron shugabannin MDA daban-daban sun nuna nasarorin da aka samu a wuraren aiki a karkashin gwamnatin Gwamna Malam Dikko Umar Radda.



