Ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina tare da hadin gwiwar gidauniyar Noor Dubai da Safe Space Humanitarian Initiative SHASHI sun gudanar da aikin tiyatar idanu kyauta ga mutane dari biyar tare da samar da tabarau da magungunan ido ga mutane dubu 1000 a fadin jihar.
Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Radda a lokacin kaddamar da wannan atisayen ta jaddada kudirinta na ganin ta dauki nauyin sabbin ayyuka da za su ciyar da al’umma gaba musamman mata da yara da tsofaffi da kuma nakasassu.
A nasa jawabin kwamishinan lafiya Dr Musa Adamu Funtua ya yaba da wannan karimcin tare da godewa kungiyoyin bisa kokarinsu.
A farkon jawabin maraba Babban Manajan Katin Katsina Eye Centre ya yi fatan wadanda suka amfana cikin gaggawar samun lafiya tare da nuna jin dadinsu da wannan karimcin.
A jawabansu daban daban wakilin gidauniyar Noor Dubai Dr Mansir da babban sakataren hukumar lafiya matakin farko Dr Shamsudeen Yahaya da sauran su sun yi jawabai sosai kan yadda ake kula da masu fama da matsalar ido.




