





Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samu wakilcin babban tawaga a jiya a wajen bikin nada rawani mai dimbin tarihi na tsohon mataimakin shugaban kasar tarayyar Najeriya Arc. Mohammed Namadi Sambo, GCON, wanda aka baiwa sarautar Sardaunan Zazzau.
Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ne ya gabatar da bikin a fadarsa da ke Zariya.
Tawagar jihar Katsina ta samu jagorancin mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin masarautu Hon. Usman Abba Jaye Danmalikin Katsina. Sauran ‘yan tawagar sun hada da Karshin Katsina da Hakimin Shinkafi, Alhaji Sanusi Kabir Usman; Sarkin Fuloti na Katsina, Alhaji Iro Idris Danfuloti; Alhaji Sadik; da sauran manyan baki da dama.
Da yake jawabi a madadin Gwamna Radda, tawagar ta mika sakon taya murna ga Arc. Mohammed Namadi Sambo a kan wannan karramawa da ya dace, inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen dan jiha wanda abin da ya gada na hidima, tawali’u da sadaukar da kai ga hadin kan kasa ke ci gaba da zaburar da shugabanni a fadin Najeriya.
Gwamna Radda, ta bakin wakilansa, ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da baiwa sabon Sardaunan Zazzau, albarka, basira, da karfin gwiwa a yayin da ya dauki wannan matsayi na gargajiya.
Bikin ya samu halartar fitattun ‘yan Najeriya, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, da masu fada a ji daga ciki da wajen kasar nan, duk sun hallara domin nuna farin cikinsu da irin gudunmawar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayar wajen ci gaban kasa da yi wa kasa hidima.