
An yi kira ga ‘yan jarida a jihar Katsina da su rungumi aikin jarida na ci gaba a cikin rahotannin su a matsayin hanyar karfafa dimokuradiyya da kuma samar da ci gaba mai dorewa a yankin.
An yi wannan kiran ne a taron lacca na kwana daya da kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina (NUJ) ta shirya, mai taken “Dimokradiyya da Ci gaban Jarida: A Case Study of Northern Nigeria”.
Laccar ta kasance wani bangare na ayyukan bukin cika shekaru 38 da kafuwar jihar Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Malam Dikko Umar Radda, wanda Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Dakta Bala Salisu Zango ya wakilta, ya amince da muhimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen ciyar da jihar gaba.
Ya yabawa kungiyar ta NUJ bisa shirya taron don girmama zagayowar ranar haihuwar jihar.
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban NUJ na kasa, Dakta Alhasan Yahya Abdullahi, ya taya al’ummar Katsina murnar zagayowar ranar.
Ya ba da tabbacin cewa a karkashin jagorancinsa, kungiyar za ta ci gaba da ba da fifiko wajen kyautata jin dadi da bunkasar sana’ar ‘yan jarida a fadin kasar nan.
Shugaban Wazirin Ilimin Kasar Hausa, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya jaddada bukatar ‘yan jarida su bayar da tasu gudunmawar wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassan jihar.
A cikin sakon fatan alheri, Kanwan Katsina Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara, ya gode wa shugabannin NUJ na kasa bisa karrama shi da lambar yabo a yayin bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafu a Abuja.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar ta NUJ na jiha, Kwamared Tukur Hassan Dan Ali ya bayyana cewa taron laccar na daya daga cikin kokarin kungiyar na murnar cika shekara 38 a Katsina da kuma bayyana rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
Har ila yau, laccar ta gabatar da makala da Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya ya gabatar mai taken “Dimokradiyya da aikin Jarida na ci gaba a Jihar Katsina”.
