
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin daukar matakin gaggawa kan matsalar rashin tsaro a jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai biyo bayan ganawar manyan masu ruwa da tsaki da shugaban kasar, jiya a fadar gwamnati da ke Abuja.
“Kamar yadda kuka sani, mun shaida abubuwan da suka tada hankali a Katsina a ‘yan kwanakin nan, mun ga ya zama dole mu zo mu ga Mai girma Shugaban kasa, mu bayyana alhininmu tare da shi, kuma mu kwanta a gabansa kalubalen da ke fuskantarmu, mun zo ne da dattawanmu, manyan mutane daga fadin Jihar domin neman goyon bayansa da taimakonsa domin jama’armu su zauna lafiya, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba,” Gwamnan ya bayyana.
Gwamna Radda ya kuma nuna godiya ga Shugaba Tinubu kan goyon bayan da gwamnatinsa ta bayar wajen bayar da kwangilolin manyan ayyukan gyara tituna a Katsina da kuma amincewa da kudade don aiwatar da su.
Ya yi nuni da cewa, da zarar an kammala wadannan ayyuka, za su kawo sauki ga jama’a da kuma alfanun tattalin arziki.
Bugu da kari, Gwamnan ya bayyana cewa tawagar ta tabo batun aikin filin jirgin Katsina da aka yi watsi da shi, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da kammala shi domin amfanin jihar baki daya.
Da yake magana kan sakamakon taron, Gwamna Radda ya ce shugaban kasar ya mayar da martani mai kyau ga dukkan damuwarsu tare da bayar da tabbacin daukar matakin gaggawa.
“Mai girma shugaban kasa ya lura da duk damuwarmu kuma ya yi alkawarin magance su cikin gaggawa,” Gwamnan ya tabbatar.
Dangane da batun tsaro, Gwamna Radda ya lura da kwakkwaran alkawurran da shugaban kasar ya dauka, wadanda suka hada da kara yawan sojojin da za a tura jihar Katsina, da samar da karin kadarori na soji, da kuma habaka tallafin jiragen sama a yaki da ‘yan bindiga.
Hakazalika ya jaddada cewa, shugaba Tinubu ya jaddada alkawarin da ya dauka tun farko na kafa bataliyar soji a kudancin Katsina, yayin da ya kuma yi alkawarin samar da rundunar ‘yan sandan tafi da gidanka cikin gaggawa a yankin, kamar yadda Sufeto-Janar na ‘yan sanda ya tabbatar.
“Wadannan ayyukan, da zarar an aiwatar da su, za su karfafa karfin hukumomin tsaro don magance rashin tsaro a fadin al’ummominmu,” in ji Gwamnan.
Gwamna Radda ya karkare da nuna kwarin guiwar cewa sabon alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi zai samar wa al’ummar Katsina dawwamammen sauki da kuma samar da yanayi mai aminci ga harkokin zamantakewa da tattalin arziki su ci gaba.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
3 ga Satumba, 2025