
Kungiyar Lajnatul HISBA ta Najeriya reshen jihar Katsina ta gudanar da taron wayar da kan jama’a kyauta a Jan-Bango Quarters dake cikin birnin Katsina.
Da yake zantawa da manema labarai gabanin fara atisayen da aka gudanar a Masallacin Abdullahi Bin Masud, Shugaban Kwamitin Lafiya na HISBA Malam Muhammad Rabiu Garba ya ce an shirya taron ne a wani bangare na ayyukan jin kai na kungiyar.
Malam Muhammad Rabiu ya bayyana cewa suna ba marasa lafiya 2000 aikin jinya kyauta kuma za a ba su magunguna yayin shirin.
Shima da yake nasa jawabin, sakataren kungiyar Malam Mustapha Abubakar ya ce a shekarar da ta gabata sun shirya irin wannan taron ga al’ummomi biyar a karamar hukumar Katsina.
Malam Mustapha Abubakar ya bayyana cewa manufar shirin ita ce a taimaka wa marasa galihu da zawarawa da marayu a cikin al’umma.
Da yake tsokaci kan shirin, shugaban kungiyar likitocin, Nas. Abdullahi Muhammad Zango ya ce tawagar ta kunshi dukkan ma’aikatan lafiya.
A jawabin godiya, Kwamandan kungiyar na shiyyar Katsina, Malam Muhammad Mahadi Rabiu Jibia, ya godewa rundunar Lajnatul HISBA ta jiha bisa zabar su da aka yi.
A wata tattaunawa da suka yi da wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin kiwon lafiya kyauta, Abdulaziz Bilyaminu da Halima Yusuf sun godewa kungiyar bisa wannan karimcin tare da yin kira ga sauran jama’a da su yi koyi da su.


