
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Katsina Ibrahim Kaula Mohammed ya sanya wa hannu kuma aka mika wa Katsina Mirror.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya yi wani dan karamin hatsarin mota a yammacin yau a kan hanyar Daura zuwa Katsina, a lokacin da yake gudanar da ayyukansa na yi wa al’ummar jihar Katsina hidima.
Mun yi farin cikin tabbatar da cewa Gwamnan na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, ba tare da wani mugun rauni da ya samu ba.
Gwamna Radda ya ci gaba da kasancewa cikin farin ciki tare da mika godiyar sa ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi kariya, da kuma al’ummar Katsina da masu hannu da shuni bisa addu’o’i da damuwa.