
An binne gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura, jihar Katsina.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta mika sakon ta’aziyyarta ga al’ummar jihar Katsina, da ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya bisa rasuwar tsohon shugaban kasar.
Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda da matarsa Hajiya Zulaihat Dikko Radda ne suka tarbe ta a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina.
Sanata Oluremi ya samu rakiyar matar mataimakin shugaban kasa, shugaban kungiyar mata ta kasa (NCWS), da matan gwamnonin jihohin Adamawa, Yobe, Ogun, Kebbi, Osun, Imo da Rivers, da kuma matan wasu ministocin tarayya.
Ta bayyana marigayi shugaba Buhari a matsayin shugaba mai tarbiya kuma mai bin ka’ida, ta ce ya tsaya tsayin daka kan dabi’unsa na sauki da rikon amana da kuma sadaukar da kai ga jama’a.
Uwargidan shugaban kasar ta yi addu’ar Allah ya jikan shi da rahama, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.
A yayin ziyarar, mai martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Faruq Umar, ya tarbi tawagar a fadarsa tare da yi musu fatan Allah ya dawo da su lafiya.