
Hukumar gudanarwar Katsina United Fc ta tsawaita dakatar da dukkan ayyukanta zuwa ranar Laraba 16 ga watan Yuli 2025.
Kungiyar ta kuma dage taron tun farko da ta yi da ‘yan wasan jihar zuwa ranar Laraba 16 ga watan Yuli 2025 bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari.
Ana sanar da duk ’yan wasan da aka gayyata cewa za a yi taron ne a ranar Laraba da karfe 2 na rana a sakatariyar kungiyar da ke cikin harabar filin wasa na Muhammadu Dikko Katsina.
Hakazalika kungiyar zata cigaba da gudanar da ayyukanta na horaswa a safiyar yau Laraba kamar yadda hukumar gudanarwa ta umarta.
Hukumar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban kasar tare da addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da Jannatul fiddausi.