
Kwamishinan wasanni na jihar Katsina Aliyu Lawal Zakari Shargalle ya mika filin wasa na garin Samaila Isah Funtua ga kamfanin Space & Dimensions Limited, wani kamfanin gine-gine na jihar domin gyara gaba daya.
Aliyu Lawal Zakari ya mika takardun aikin filin wasan ga shugaban kamfanin Engr. Abu Kasim, a wani taron da aka gudanar a filin wasan.
A cewar kwamishinan wasanni, gwamnatin jihar mai ci ta Dikko Umar Radda ta amince da inganta filin wasan saboda mahimmancin da yake da shi wajen karfafa harkokin wasanni a jihar.
Kwamishinan wasanni ya bayyana cewa sassan aikin sun hada da sake tayar da katangar filin wasan, da gina magudanun ruwa, da sanya ciyayi, da kuma hanyar guje-guje da tsalle-tsalle.
Aikin yana da tsawon watanni hudu da ya fara a yau.
A nasa jawabin, Engr. Abu Kasim, Babban Jami’in Kamfanin Space & Dimensions Limited, ya godewa Gwamna Dikko Radda bisa amincewar sa wajen gudanar da aikin. Engr. Abu Kasim ya ba da tabbacin cewa za a gina filin wasan yadda ya dace kuma zai dauki tsawon lokaci mai tsawo.
Engr. Kasim, Babban Jami’in Kamfanin Space & Dimensions Limited, ya nanata kudirin kamfanin na kammala inganta filin wasan cikin wa’adin da aka kayyade.
An bayar da kwangilar ne a kan kudi naira miliyan casa’in da tara.