
Gwamnatin jihar Katsina ta yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa cibiyoyin koyon sana’o’in hannu na al’umma domin su kara kaimi kan shirye-shiryen rage radadin talauci.
Kwamishinan ma’aikatar fasaha da koyar da sana’o’i Alh Isah Muhammad Musa ya bayyana hakan a ci gaba da rangadin da ya kai cibiyoyin koyon sana’o’i na jiha.
Alh Isah Musa wanda ya jagoranci tawagar ma’aikatar zuwa cibiyar koyar da sana’o’in gargajiya ta Mani, ‘Cosdac’ ya sanya ido kan yadda ake gudanar da jarabawar karshe ta cibiyar tare da yin kira ga daliban da suka koyo da su rubanya kokarinsu na dogaro da kai.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta umarci manyan makarantun jihar da su tabbatar da farfado da harkokin kasuwanci a cibiyoyinsu.
Ya kuma umurci daliban da su koyo da su mayar da hankali sosai kan sana’o’insu ko da bayan sun kammala karatunsu domin inganta tattalin arzikinsu don bayar da gudunmawarsu ga ci gaban jihar.
Domin kwadaitar da daliban cibiyar kwamishina ya bada kwangilar dinkin kayan Sallah da za a rabawa marayun da aka zaba kyauta domin bikin Sallah.
Kwamishinan ya yi alkawarin bayar da tukuicin tuhume-tuhume ga daliban da suka kware sosai, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa wa cibiyoyin koyon sana’o’i a yankunansu domin ci gaban tattalin arzikin jihar da ma kasa baki daya.